Dokoki Na Bangaran Sana'o'i.

 

Dokokin v

 ASSALAMU ALAIKUM Taken M&B .Babu maraya sai rago .Babu marainiya sai raguwa .Babu marayu sai ragwaye .M&B Gaskiya Da gaaskiya .M&B Keke da keke shugaban M&B [watau chairman] comrd. muh'd umar dan barde, ina matukar murnar tayaku murnar shigowarku m&d indai harhar kun amince da dokokin mu kuje website ku ciro admission latter tare da i.d card bayn nan zaku dawo head office ku bude file, alokacin ne za,a fada muku ranar da zaku fara zuwa. ina mai baku shawara ku rike admission latter da scrash card dinku da muhimmanci, domin idan kun gama koyan sana,oin baza,a baku shaidar kammalawa ba [watau certificate] sai da shi kuma duk wanda ya samu nasarar samun shaidar kammalawa [certificate] zai iya shiga ko ina a nigeria kuma adaukeshi n aioki da ita. shi ne yasa nake bada shawara agareku , da ku tsaya kuyi abinda kuka zo yi na koyan sana'o'i domin ku dogara da kanku ina fatan zaku kiyaye mana dokokinmu kamr haka: 1- [A] Zaka/ki yi kwafi na wannan admission, form da garanto kowanne biyu, [B] Daya zaka/ki bayar ga shugabannin da suka kawoka/ki domin su ajiye a fayil [file] dinsu. [C] Dayar kuma zaka/ki tawo dasu head office tareda takardun makaranta sai arubuto, dasune za'a bude maka/ki [file] 2- [A] Ba ayarda dalibi ko daliba ya shigo harabar makarantaba saida shiga ta kamala da mutunci [B] Irin wacce addininmu ya yarda da ita hijabi kuma ya zama fari da kore a samansa 3- [A] kungiyoyinda suka hadu suka zama M&B babu maraya sai rago sunaso duk wani dalibi ko daliba dayaga wani abu yana faruwa a unguwarsu, ko wani waje da idonsa yakai gareshi, da ya gaggauta ya sanar damu [B] Donmu sanar da hukumar da ya kamata a sanarwa. 4- [A] Ba'a son makara, kafin minti 20 lokacin shiga ajinku yayi mukeso kowa yazo don kowanne group su tattauna akan abinda aka koya musu jiya kuma su ware assignment din da zasu bayar a aji. [B] In har ka makara masu kula da zirga zirga zasu karbi kudin makara naira 20 in kuma halin mutum ya zama mai yawan makara zasu kawo mana kai/ke office don musan hukuncin da zamu dauka. 5- [A] Idan ka/ki zo makaranta ka/ki shiga ajinku, [B] hakama idan an tashi ba'aso wani dalibi ko daliba su tsaya indai ba da sanin hukumar makaranta ba, a tafi gida kawai. 6- [A] Babban laifine ganin wani dalibi a filin makaranta. [B] Yan aji biyu kuma su tabbata sun tsaya a wajen da aka tanadar musu ba tare da surutu ko hayaniya ba, saboda su doka tafi tsanani akansu. 7- [A] Babu zuwa da yaro ko na goye ne saidai a tawo da mai raino wanda masu kula da gate zasu nuna wajen da zasu tsaya. [B] Sabada idan yaro yayi kuka a aji zai bayar da matsala. 8- [A] Idan za'a shiga aji a tabbatar ankashe waya ko a sata a silent,domin ba'a son surutu ko kadan. 9- [A] Wajibi ne dalibi ya yiwa malami biyayya ya kuma girmama shi da kuma bin umarnin da ya bayar. 10-Babban laifine aci abinci ko asha abinsha a cikin aji. 11-Wajibine a kiyaye siye ko siyarwa a cikin aji dama  makaranta gaba daya. 12-Wajibine abi umarnin da jami'an tsaro da masu gadi da kuma masu kula da zirga zirgar makaranta suka bayar. 13-[A] Duk wanda yake da wata matsala ya sanar da shugabannin ajinsu [wato monitor], [B] Shikuma monitor ya sanarda malami, [C] Idan ba'a magance matsalarba a gaggauta sanar da babban office dinmu ko ya rubuto asa a cikin akwatin korafi. 14- [A] Monitor da mataimakinsa da shugabannin group [wato group leaders] na kowanne aji ne suke da hakkin marawa monitor da malami baya, a duk abin da ake aiwatarwa. [B] Muddin dai abin yana cikin tsarin dokokin M&B Babu maraya sai rago. 15- [A] Muna masu sanar daku cewa duk wani dan aji daya da yayi fashin kwana uku to ya kori kansa da kansa, [B] Su kuma "yan aji biyu idan suka yi fashin kwana biyu suma sun kori kansu da kansu, [C] Amma idan akwai babban uziri to sai a rubuto abinda yake faruwa a bayan copy din admission letter a kawo kafin kwanakin su cika. 16- [A] Duk wanda yazama dalibinmu saiya yarda da cewa zai zama mai kishin kayayyakin da muke samarwa a cikin gida nigeria, [B] Kuma ya zama mai amfani dasu. 17- [A] Muna sanarda dalibi cewa adaure a tanadi kudin handout da attestation form kudinta yan center waje 870, [B] Amma ta computer da makeup 1070, [C] Ta yan head office 1070 amma su tasu ta computer ce da makeup 1200. [c] ta masu karatun diploma da H.N.D tasu 1500. 18- [A] wajibi ne dalibinmu ya guji yada jita-jita koda kuwa ba abangaren makaranta ba ne [B] bamu yarda dalibinmu ayi magana dashi ba ko a wata kafar sadarwa ba ba tare da izininmu ba don yin hakan babban lafi ne [C] idan kana/kina da korafi asanar damu ta hanyar da tadace, kamar yadda muka fada a sashi 13,14,15 19- [A] muna sanar daku cewa akwai shugabanin dalibai a ko wacce center [B] Suna lura tare da sa'ido akan abinda ya sabawa dokokin M&B, kamar yadda muke da sss acikin dalibai 20- [A] Sannan dole ne duk wacce tazo bakin makaranta ta cire niqabin fuskarta [B] saboda kaucewa zargin aikata ba dai-dai ba 21-muna masu sanar daku cewa : [A] Zakuzo head office sau biyu: watan farko zakuzo da kudin jarabawa 100 ranar defending project bayan wata biyu zuwa uku da yin jarabawarku a ranar zaku sayi clearance form wadda shaidar mun rabu daku lafiya, daga nan za,a saka muku copy a file se a baku original daga nan se a mayar da file dinku office din masu fitar da certificate [C] alokacin zaka tsaya idan kana da lokaci acire maka certificate a website. 22- [A] Duk karshen wata wajibi ne zuwa semina ga duk wani dalibi rashin zuwansa zaisa adauki makataki akansa [B] ranar semina za,a gabatar da abubuwan da ba su kuke koya ba amma wadanda muka tabbatar zaku amfana dasu shi yasa ma don a gudanar da pratical dinsu kowa zai tawo da 100 'yan makeup da 'yan girki da kuma masu diploma da HND sukuma 200 don a samar da wadatattun kayan practical 23- muna iya canja doka in har bukatar hakan ta taso amma a rubuce kamar haka 24- idan abu ya faru kuma babu hukuncinsa a cikin dokoki [B] national chairman zai iya daukar dokar da ta dace kafin a shigar