About

About

Kungiyoyi ne da yawa masu son cigaban Wannan Al’umma, Suka dunkule waje Daya Domin Ceto Wannan Al’ummarmu daga halin da ta fada. Bayan Dogon Nazari da tattaunawa muka ga cewa rashin aiki ko kuma sana’a shine jagora wajen bawa wannan Al’umma matsaloli. Don Haka muka tsaida matsaya daya, itace Daukan Sano’oin Hannu Muke Koyar dasu a aikace a kokarin mu na ganin cewa mun nesanta ‘yan Nijeriya daga matsalar rashin aikinyi da dogaro da Kai. Mun Samu nasarori masu yawan gaske tun farkon farawar mu a shekara ta 2012 har zuwa sanda Kungiyoyin mu Suka Dunkule a Shekarar 2015, Wanda Hakan Ya Sanya Muka ga dacewar yiwa Kungiyar mu Rijista da Gwamnati, wanda hakan Ya faru a shekara ta 2016.

Daga Cikin Nasarorin da mu ka samu sun hada da:

  1. Koyar da Sano’o’in Hannu Kala Daban-daban Ga Matasa Masu Yawan gaske kuma kyauta.
  2. Sayan Kayan Da Wadannan Matasa suka sarrafa daga wajensu.
  3. Tallata tare da siyar da hajjojin da Dalibanmu suka Sarrafa.
  4. Bada Gudunmawa ga Matasa da Yawa, Kama daga Birni Har zuwa Kauyuka.
  5. Da Bijiro da sabbabbin hanyoyin samun aikinyi da dama.